logo

HAUSA

An shirya tattaunawar shugabanni kan makomar Sin da Afirka karo na farko ta kafar bidiyo

2021-11-08 10:20:12 CRI

An shirya tattaunawar shugabanni kan makomar Sin da Afirka karo na farko ta kafar bidiyo_fororder_dandali

Jiya Lahadi 7 ga wata, kungiyar sada zumunta tsakanin Sin da kasashen waje ta kasar Sin ta shirya “tattaunawar shugabanni kan makomar Sin da Afirka karo na farko” ta kafar bidiyo domin ingiza cudanyar dake tsakanin matasan sassan biyu wato Sin da Afirka, inda shugaban kungiyar Lin Songtian ya bayyana cewa, matasan Sin da Afirka, fatan sassan biyu ne, suna taka muhimmiyar rawa wajen ingiza hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka.

A nasa bangaren, wakilin kungiyar AU dake kasar Sin Rahamtalla Mohamed Osman shi ma ya bayyana cewa, ya yi farin ciki matuka sakamakon yadda tattaunawar ta samu halartar wakilan matasan Sin da Afirka kusan 300.

A matsayinta na aminiyar kasashen Afirka, cikin dogon lokaci, kasar Sin tana taimakawa ci gaban matasan kasashen Afirka ta hanyoyin more ilmomi da cudanyar al’adu. Za a kira taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin a Senegal a karshen watan nan da muke ciki, ya dace matasan Sin da Afirka su kara ba da gudummowarsu. (Jamila)