logo

HAUSA

MDD ta yi tir da yunkurin kisan Firaministan Iraqi

2021-11-08 11:36:17 CRI

MDD ta yi tir da yunkurin kisan Firaministan Iraqi_fororder_211108-UN chief-Faeza3

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da yunkurin kisan Firaministan Iraqi Mustafa al- Kadhimi, a ranar Lahadi.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa Staphane Dujarric ya fitar, sakatare janar din ya yi kira da a tabbatar da kama wadanada ke da hannu, yana mai bukatar al’ummar kasar su kai zuciya nesa, su kuma bijirewa duk wani rikici da ka iya tada hankalin kasar.

Sakatare Janar din ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a siyasa, su girmama kundin tsarin mulkin kasar da warware sabani cikin ruwan sanyi da gudanar da tattaunawar da za ta kunshi kowa da kowa. (Fa’iza Mustapha)