logo

HAUSA

Shugaban rundunar sojin Sudan ya tabbatar da zai mika mulki ga farar hula

2021-11-08 09:40:40 CRI

Shugaban rundunar sojin Sudan ya tabbatar da zai mika mulki ga farar hula_fororder_211108-Sudan-Faeza1

Shugaban rundunar sojin Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya jaddada kudurinsa na mika muki ga farar hula a kasar.

Abdel Fattah Burhan, ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi tawagar kungiyar kasashen Labarawa karkashin jagorancin Sakatare Janar na kungiyar Hossam Zaki.

Gidan talabijin na kasar ya ruwaito shugaban na cewa, rundunar sojin ta kuduri niyyar rike mulki zuwa lokacin da za a gudanar da zabe, jama’a su zabi gwamnati.

A nasa bangare, Hossam Zaki ya jaddada muhimmancin tattaunawa a tsakanin bangarorin kasar domin cimma mafita mai gamsarwa ga kowanne bangare.

Ya kuma kara da cewa, a shirye kungiyar ta kasashen Larabawa take, ta taimakawa bangarorin kasar Sudan din hawa teburin sulhu. (Fa’iza Mustapha)