logo

HAUSA

Jami’in Rwanda: CIIE muhimmin dandalin ciniki da zuba jari ne

2021-11-07 16:17:52 CRI

Jami’in Rwanda: CIIE muhimmin dandalin ciniki da zuba jari ne_fororder_a02-CIIE offers excellent platform for trade

Wani jami’in kasar Rwanda ya ce, bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin wato CIIE, wanda ke gudana a halin yanzu, ya samar da muhimman damammakin kasuwanci da zuba jari a kasuwa ta biyu mafi girma a duniya.

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Juma’a, Diane Sayinzoga, shugaban sashen kula da kayayakin da kasar ke fitarwa ketare a hukumar bunkasa ci gaba ta kasar Rwanda RDB, ya bayyana cewa, baje kolin CIIE ya kasance a matsayin wani kyakkaywan dandalin nune nunen kayayyaki, da cinikayya, da kuma zuba jari.

A wajen bikin na CIIE karo na hudu, wanda ke gudana a Shanghai tsakanin 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba, wasu kamfanoni hudu na kasar Rwanda sun halarci bikin, inda abokan huldarsu Sinawa suka wakilce su ta hanyar kafa rumfuna ta kafar bidiyo.

A bikin baje kolin na wannan karo, kasar ta tsakiyar Afrika ta kawowa Sinawa masu sayayya wasu ingantattun kayayyaki daga kasar Rwanda, wadanda suka hada da koffee, da ganyen shayi, da yaji, da man avocado, da sauransu. Jami’in ya ce, wannan karo na hudu ke nan da kasar Rwandan ke halartar baje kolin na CIIE.

Sayinzoga ya ce, baje kolin zai taimakawa kamfanonin kasar Rwanda wajen fahimtar karin nau’o’in kayayyakin da ake bukata a kasuwannin kasar Sin baya ga koffee da ganyen shayi da ta kasar ta jima tana fitarwa zuwa kasar Sin. (Ahmad Fagam)