logo

HAUSA

An ceto mutane 6 da aka sace daga jami’ar Abuja ta Nijeriya

2021-11-06 17:04:54 CRI

An ceto mutane 6 da aka sace daga jami’ar Abuja ta Nijeriya_fororder_4ec2d5628535e5ddcc7afef6e408fae6cf1b6298

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta ce an kubutar da mutane 6 da wasu ‘yan bindiga suka sace daga jami’ar Abuja, da ke babban birnin kasar a farkon makon da ya gabata.

Wasu gungun ‘yan bindiga ne suka sace mutanen da suka hada da ma’aikata 4 da yara biyu na daya daga cikin ma’aikatan, a lokacin da suka kai hari gidajen ma’aikatan jami’ar dake wajen birnin Abuja da safiyar ranar Talata.

Cikin wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan ta ce an ceto mutanen ne a jiya Juma’a, ta hanyar hadin gwiwa tsakaninta da sauran hukumomin tsaro.

Cikin wata sanarwa ta daban kuma, shugaban jami’ar Abdul Rasheed Na’Allah ya bayyana cewa, za a duba lafiyar mutanen domin tabbatar da suna cikin koshin lafiya, kafin a sada su da iyalansu. (Fa’iza Mustapha)