logo

HAUSA

Kasar Sin tana nacewa ga tsarin huldar kasa da kasa

2021-11-05 14:23:16 CRI

Kasar Sin tana nacewa ga tsarin huldar kasa da kasa_fororder_211105-MDDSIN

Gomman jami’an MDD da jakadu daga kasashe da dama ne suka halarci bikin nune-nunen hoton domin cika shekaru 50 da dawowar kujerar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a MDD.

Ofishin jakadancin kasar Sin da na MDD dake Geneva da kuma kamfanin dillancin labarai na Xinhua ne suka shirya nune-nunen wanda aka yi wa lakabi da “Inganta ci gaba na bai daya domin makoma mai haske.”

Darakta Janar na ofishin MDD a Geneva, Tatiana Valovaya, ta ce cikin shekarun 50 da suka gabata, kasar Sin ta samu dimbin nasarori, tana mai cewa ana ganin rawar da Sin din ke takawa a MDD.

A nasa bangaren, zaunannen wakilin Isra’ila a ofishin MDD dake Geneva, Meirav Eilon Shahar, ya ce ya kamata dukkan kasashe su kasance tare yayin da ake fuskantar kalubale ko barazana a wannan zamani.  (Fa’iza Mustapha)