logo

HAUSA

Charlie Munger ya fifita manufofin tattalin arzikin kasar Sin kan na Amurka

2021-11-05 16:02:00 CRI

Charlie Munger ya fifita manufofin tattalin arzikin kasar Sin kan na Amurka_fororder_211105-推送-hoto2

Yayin wata tattaunawa da kafar watsa labarai ta CNN a ranar 3 ga wata, mataimakin shugaban kamfanin Berkshire Hathaway dake Amurka Charlie Munger, ya ce mahukuntan kasar Sin sun aiwatar da matakai masu ma’ana, sama da na Amurka a fannin bunkasa tattalin arziki. Munger ya ce Sin ta hango matsalolin dake tunkarowa, tare da daukar matakan shawo kansu a lokacin da tattalin arzikin take bunkasa. Ya kuma jinjinawa kwazon kasar Sin na shawo kan karuwar yawan al’ummarta a kan lokaci, da kuma nasarar da ta cimma ta fitar da kusan al’ummun ta biliyan 1 daga kangin talauci.   (Saminu)