logo

HAUSA

Shirin muhalli na MDD: Galibin kasashe na da karancin kudaden tinkarar sauyin yanayi

2021-11-05 10:27:27 CRI

Shirin muhalli na MDD: Galibin kasashe na da karancin kudaden tinkarar sauyin yanayi_fororder_211105-sy-A1

A ranar 4 ga watan Nuwamba, shirin kare muhalli na MDD ya fidda rahotonsa na ayyukan kare muhalli na shekarar 2021. Rahoton ya yi nuni da cewa, duk da karuwar da ake samu na shirye-shirye da manufofin dake shafar yaki da matsalolin sauyin yanayi, amma hakikanin kudade da ake bukata da yanayin ci gaban da ake samu wajen aiwatar da shirye-shirye har yanzu ba su kai matakin da ake bukata ba. Galibin kasashen duniya ba su yi kyakkyawan amfani da damammakin farfado da tattalin arzikinsu bayan fama da yaduwar annobar COVID-19 ba, kuma sun gaza cimma bayar da fifiko wajen bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba yayin da suke kokarin karfafa aiwatar da tsare tsaren yaki da matsalolin sauyin yanayi kamar matsalar fari, da mummunar iska, da wutar daji.

Inger Andersen, babbar daraktar shirin kare muhalli ta MDD, ta bayyana cewa, “duniya ta lashi takobin kara rungumar amfani da makamashi mai tsafta don rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, amma kokarin da suke bai wadatar ba. A halin yanzu, tilas ne kasashen duniya su rungumi tsarin yaki da matsalar sauyin yanayi. Ya kamata a yi kokarin cimma nasarar kawo sauye sauye wajen samar da kudade da kuma aiwatar da shirin yaki da matsalar sauyin yanayi, kana a kara bijiro da wasu muhimman manufofi, domin a cimma nasarar rage illoli da hasarorin da matsalar sauyin yanayi ke haifarwa. Ya kamata mu yi aiki tukuru ba tare da jinkiri ba,” inji jami’ar. (Ahmad)