logo

HAUSA

Yan kasuwar Syria na fatan kara shiga kasuwannin Sin ta hanyar amfani da dammakin baje kolin CIIE

2021-11-05 10:36:55 CRI

Yan kasuwar Syria na fatan kara shiga kasuwannin Sin ta hanyar amfani da dammakin baje kolin CIIE_fororder_211105-CIIE-S2

’Yan kasuwar Syria sun bayyana fatansu na kara shiga kasuwannin Sin, ta hanyar amfani da dammakin da baje kolin CIIE ya tanadar, na baje hajoji ga babbar kasuwar kasar Sin.

Da take tsokaci kan hakan, ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Damascus, mai kamfanin BioCham Ali-Adeeb, ta ce za su ci gaba da halartar baje kolin na CIIE duk shekara, bayan da suka sayar da dukkanin hajojin su da suka baje.

Shi ma Yassin Diab, manajan shiyya na kamfanin Serjella dake kasuwancin albarkatun man zaitun, cewa ya yi fatan su shi ne kara tallata hajojin su ga babbar kasuwar kasar Sin. Mr. Diab ya kara da cewa "Muna kallon kasar Sin a matsayin babbar kasuwar mu ta sayar da hajoji." (Saminu)