logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a samar da mafitar siyasa dangane da rikicin Sudan

2021-11-05 10:17:21 CRI

MDD ta yi kira da a samar da mafitar siyasa dangane da rikicin Sudan_fororder_211105-Sudan-F2

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci Abdel Fattah al-Burhan, shugaban rundunar sojin Sudan, ya lalubo mafita a siyasance, domin shawo kan rikicin dake wakana a kasar.

Da yake zantawa da Abdel Fattah Burhan ta wayar tarho a jiya, Antonio Guterres ya jaddada cewa, MDD za ta ci gaba da tsayawa tare da al’ummar Sudan, yayin da suke kokarin cimma burinsu na samun zaman lafiya da ci gaba da dorewar demokradiyya.

A ranar 25 ga watan Oktoba, rundunar sojin Sudan ta rushe gwamnatin riko na hadakar farar hula da soji, inda ta tsare Firaminista Hamdok da ministocinsa. (Fa’iza Mustapha)