logo

HAUSA

Shugaban Tunisia ya sha alwashin daukar matakai mafi dacewa a kasarsa

2021-11-05 10:46:33 CRI

Shugaban Tunisia ya sha alwashin daukar matakai mafi dacewa a kasarsa_fororder_211105-Tunisya-A2

Shugaban kasar Tunisia Kais Saied, ya sanar cewa, ya lashi takobin gaggauta daukar kwararan matakan da ya ayyana a ranar 25 ga watan Yuli.

A jawabin da ya gabatar yayin taron majalisar ministocin kasar, Saied, ya nanata kudirinsa na tabbatar da kare hakkoki da ’yancin dukkan ’yan kasar, bisa dacewa da dokokin tsarin mulkin kasar.

A ranar 25 ga watan Yuli, shugaban kasar Tunisia ya sanar cewa, ya sauke Hichem Mechichi, daga mukamin firaministan kasar, kana ya dakatar da dukkan ayyukan majalisar wakilan jama’ar kasar, ko kuma majalisar dokoki ta kasa. A ranar 29 ga watan Satumba, ya nada Najla Bouden, a matsayin sabon firaministan kasar. (Ahmad)