logo

HAUSA

AU ta yi kira da a gaggauta tsagaita rikici a Habasha

2021-11-04 10:33:49 CRI

AU ta yi kira da a gaggauta tsagaita rikici a Habasha_fororder_211104-faiza-1-Faki

Shugaban hukumar AU Musa Faki Mahamat, ya bayyana matukar damuwa dangane da ta’azzarar ayyukan soji a Habasha.

Wata sanarwa da AU ta fitar, ta ruwaito shugaban na kira da a tsagaita bude wuta, sannan a girmama rayuka da dukiyoyin fararen hula tare da kayayyakin gwamnati. Haka kuma ya bukaci bangarorin dake rikici su hau teburin sulhu domin lalubo hanyoyin warware matsalolinsu domin ci gaban kasar.

Har ila yau, Moussa Faki Mahamat ya bukaci bangarorin su kiyaye cikakken ’yanci da yankunan kasar da hadin kan al’ummarta.

Ya kara kira ga bangarorin su gargadi magoya bayansu game da ramuwar gayya kan kowacce al’umma da kauracewa kalaman kiyayya da ingiza rikici da rarrabuwar kawuna

Ya kuma jaddada cewa, AU na nan kan bakanta na ci gaba da hada hannu da dukkan bangarorin domin cimma matsayar siyasa guda. (Fa’iza Mustapha)