logo

HAUSA

Riga kafin kasar Sin ya taimakawa kasashe marasa karfi

2021-11-04 15:50:16 CRI

Riga kafin kasar Sin ya taimakawa kasashe marasa karfi_fororder_211104-faiza-4-allurai

Jaridar Nature ta wallafa wani sharhi a ranar 1 ga watan Nuwamba, inda ta ce kasar Sin ta fara fitar da adadi mai yawa na riga kafin COVID-19 tun da wuri. Inda kawo yanzu, ta tura sama da allurai biliyan 1.1 zuwa kasashe da yankuna 120 dake fadin duniya. A cewar sharhin, riga kafin kasar Sin ya samar da muhimmin tallafi ga kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga. Lamarin ya sha bambam da Amurka da ta fara bayar da gudunmuwa a watannin baya-bayan nan, inda zuwa 21 ga watan Oktoban bana, ta bayar da allurai miliyan 206 kawai. (Faeza Mustapha)