Bikin CIIE ya nuna tunanin kasar Sin na “Mu more tare”
2021-11-04 17:40:21 CRI
Yau ne za a kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin(CIIE) karo na 4 a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda wasu kamfanoni kimanin 3000, na wasu kasashe da yankuna 127 za su nuna sabbin nau’ikan kayayyaki da fasahohinsu.
Bikin CIIE ya kan janyo hankalin ‘yan kasuwan kasashen Afirka, saboda wadanda aka shirya a baya ya ba masu fasahar saka duwatsu na kasar Zimbabwe damar kulla huldar hadin kai tare da wasu mutanen kasar Sin, da sanya ruwan zuma kirar kasar Zambia shiga cikin kantunan sayar da magani fiye da 50 dake birnin Shanghai, gami da taimakawa kamfanonin samar da busashen yaji na kasar Rwanda samun damar sayar da yajin har ton dubu 10 a kasuwannin kasar Sin duk shekara.
Sai dai mene ne ainihin ma’anar bikin CIIE?
Wannan biki daya ne daga cikin nau’o’in bukukuwan baje kolin kayayyaki. Bikin bajekolin kaya tamkar wata babbar kasuwa ce, inda ake samun ‘yan kasuwa da yawa da suke sayar da kayayyakin su. Sai dai bikin baje kolin kaya da aka fi ganinsa shi ne bikin baje kolin kayayyakin da ake son fitar da su zuwa kasashen waje, inda ake neman janyo hankalin mutanen kasashen waje domin su sayi karin kayayyakin wata kasa. Sai dai bikin CIIE ya zama akasin haka, domin shi wani nau’in bikin ne da ake gayyatar ‘yan kasuwa na kasashen waje, don taimaka musu sayar da kayayyakinsu ga mutanen gida. Wato ana taimakawa al’ummun kasashen waje samun riba ke nan. Amma me ya sa kasar Sin take so ta shirya wani biki irin wannan?
Da farko, bikin CIIE ya dace da manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje. Kasar Sin ta taba fama da koma bayan tattalin arziki, daga baya ta fara daukar manufar bude kofarta don janyo hankalin kamfanonin kasashen waje, wadanda suka zo kasar Sin domin zuba jari, tare da samun riba. A sa’i daya, wannan dabara ta sa kasar Sin samun kudi, da fasahohi, ta yadda ta raya masana’antunta sannu a hankali. Saboda haka, kasar Sin ta fahimci muhimmancin bude kofarta ga kamfanonin ketare, gami da hadin gwiwa da su.
Na biyu, shi ne domin ra’ayin kasar Sin da ya shafi maganar adalci da moriya. Bisa al’adun kasar Sin, ya kamata a samu daidaituwa tsakanin batun adalci da moriya, wato a tabbatar da daidaito tsakanin yadda ake amfanar saura, da yadda ake morar kai. A ganin Sinawa, dole ne a samu wannan daidaito, kafin a iya tabbatar da dorewar wata huldar hadin gwiwa.
Na uku, shi ne neman daidaita yanayin ciniki na kasa da kasa. A halin yanzu, annobar COVID-19 ta haddasa koma bayan tattalin arzikin duniya, da sanya wasu kasashe, musamman ma masu wadata, neman kare kansu ta hanyar tanada kayayyaki a gida, da takaita ciniki, ba tare da lura da bukatu na sauran kasashe ba. Saboda haka, kasar Sin na neman bude kasuwanninta, don samar da karin damammkin cudanya da hadin kai, ta yadda za a samu daidaita ra’ayin da ake samu na son “rufe kofa”.
Baya ga wadannan fannoni, wani dalili na tushe da ya sa kasar Sin karbar bakuncin bikin CIIE, shi ne tunanin kasar na “Mu more tare”. Yayin da kasar Sin take hulda da sauran kasashe, ta kan jaddada bukatar “morewa tare” da “samun moriya tare”. Saboda kasar Sin ta san cewa, tsarin tattalin arzikin duniya ba wani abu ne da ke sanya wani cin moriya, yayin da saura suke hassara ba. Kana karuwar tattalin arzikin duk wata kasa ta kan kawo ci gaba ga tattalin arzikin daukacin kasashen duniya. Ban da wannan kuma, yadda ake raba moriya, da hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban, ya kan haifar da karin riba ga kasuwannin duniya, ta yadda duk wata kasa za ta more.
Muna da imanin cewa, wata rana za a kawo karshen babakere da nuna fin karfi, da yanayin kashin dankali a duniya, kana za a maye gurbin wadannan abubuwa da wani sabon yanayi na hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban, musamman ma kasashe masu tasowa, ta yadda za su ci gaba tare.
“Morewa tare” da “Cin moriya tare” ba wasu kalmomi ne na musamman ba, saboda a kan ji su yayin da ake cudanya tsakanin al’ummu. Sai dai wadannan kamfanonin kasashen Afirka, da suka samu damar sayar da kayayyakinsu a kasar Sin, ta hanyar halartar bikin CIIE, za su gaya maka cewa, maganar da kasar Sin ta fada ba ta fatar baki kawai ba ce, domin kuwa ainihin mataki ne da kasar ke aiwatarwa. (Bello Wang)