logo

HAUSA

MDD ta nuna matukar damuwa kan barkewar tashin hankali a Habasha

2021-11-03 09:47:55 CRI

MDD ta nuna matukar damuwa kan barkewar tashin hankali a Habasha_fororder_1103-Habasha-Ahmad

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi matukar nuna damuwa ga barkewar tashin hankali na baya bayan nan dake cigaba da karuwa a kasar Habasha da kuma dokar ta bacin da gwamnatin kasar ta kafa.

A cewar sanarwar da kakakin babban sakataren ya fitar da yammacin ranar Talata, ya ce zaman lafiyar kasar Habasha da yankuna masu yawa na kasar na fuskantar hadari.

Jami’in MDDr ya jaddada yin kira ga bangarorin dake yaki da juna da su gaggauta tsakaita bude wuta, kana su bayar da damar shigar da kayayyakin agaji don tallafawa ceton rayukan jama’a a shiyyar arewacin kasar mai fama da rikici.

Guterres, ya kuma bukaci a gudanar da cikakkiyar tattaunawa ta kasa don warware matsalolin kasar da kuma gina tubalin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin kasar.

Babbar sakatariya mai kula da sashen siyasa da gina zaman lafiya ta MDDr Rosemary DiCarlo, ta jaddada yin wannan kira. (Ahmad Fagam)