logo

HAUSA

Najeriya: Adadin wadanda ginin nan mai hawa 21 ya hallaka a Lagos ya karu zuwa mutum 20

2021-11-03 09:37:59 CRI

Najeriya: Adadin wadanda ginin nan mai hawa 21 ya hallaka a Lagos ya karu zuwa mutum 20_fororder_1103-Lagos-Saminu

Jami’in tsare tsare na hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya a jihar Lagos dake kudancin kasar Ibrahim Farinloye, ya ce ya zuwa ranar Litinin, adadin gawawwakin da aka tono karkashin baraguzan ginin nan mai hawa 21, na unguwar Ikoyi ta jihar ta Lagos ya karu zuwa mutum 20.

Farinloye wanda ke bayyana halin da ake ciki, don gane da aukuwar wannan ibtila’i cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, ya ce ana ci gaba da zakulo karin gawawwaki daga sassan ginin, ko da yake ba a kai ga tantance adadin wadanda ginin ya binne ba.

Jami’in ya kara da cewa, baya ga wadanda suka rasu, jami’an aikin ceto sun yi nasarar ceto mutane 9 da ran su, yayin da a daya hannu ake fadada bincike game da musabbabin aukuwar lamarin.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kwashe sama da shekara guda ana ginin benen, kuma adadin ma’aikata musamman ma leburorin dake aikin ginin, na iya haura mutum sama da 50 a lokacin da ya rushe.

A jiya Talata, gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar ta Lagos, ya fitar da wata sanarwa, wadda a cikin ta ya sha alwashin bincikar wannan lamari. Yana mai cewa, gwamnatinsa na shirin kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa, don tabbatar da an bankado gaskiyar al’amarin.  (Saminu)