logo

HAUSA

Sama da kaso 60% na Amurkawa ba su gamsu da yanayin tattalin arzikin kasar ba

2021-11-03 11:03:03 CRI

Sama da kaso 60% na Amurkawa ba su gamsu da yanayin tattalin arzikin kasar ba_fororder_src=http___pic1.zhimg.com_v2-809951de887c97f8d44964788220ade5_1440w_source=172ae18b&refer=http___pic1.zhimg

Kafar yada labarai ta AP dake Amurka, ta gabatar da sakamakon jin ra’ayin jama’a a kwanan baya, wanda ya nuna ra’ayin Amurkawa game da halin tattalin arzikin kasar dake kara tsananta, saboda matsalar samar da kayayyaki, da hauhawar farashi da sauransu. Rabin mutanen da kafar ta zanta da su sun yi hasashen cewa, halin tattalin arzikin kasar zai kara tsananta a badi.

Kafar yada labarai ta AP, ta kaddamar da wannan bincike na jin ra’ayin jama’a, wanda ya nuna cewa, kashi 35% na Amurkawa ne kadai suka gamsu da yanayin tattalin arzikin kasar, yayin da sauran kaso 65% na matukar nuna rashin jin dadin su.

A watan Satumba, bincike da aka yi a wannan fanni ya nuna cewa, Amurkawa kashi 45% suna ganin cewa, halin tattalin arzikin kasar na tafiya yadda ya kamata. Ra’ayin Amurkawa masu nuna rashin jin dadi kuwa, ya yi daidai da na farkon shekarar bana, lokacin da cutar COVID-19 ta fi kamari. (Amina Xu)