logo

HAUSA

Masar ta karbi sabon kaso na alluran rigakafin Sinovac

2021-11-02 11:03:18 CMG

Masar ta karbi sabon kaso na alluran rigakafin Sinovac_fororder_1102-saminu-4

A jiya Litinin ne ofishin jakadancin Sin dake kasar Masar, ya bayyana cewa, Masar ta karbi sabon kaso na alluran rigakafin cutar COVID-19 ta kamfanin Sinovac.

Cikin wata sanarwa, ma’aikatar lafiya da kididdigar yawan al’umma ta Masar, ta ce rigakafin da gwamnatin Sin ta samar, na karkashin wani shirin hadin gwiwa ne tsakanin kasashen 2, domin dakile yaduwar annobar a Masar.

Sanarwar ta kara da cewa, ya zuwa yanzu, Masar ta karbi alluran rigakafin COVID-19 sama da miliyan 74. Kaza lika kasar ta tsara yiwa baligai miliyan 40 rigakafin, nan da karshen shekarar nan ta 2021.  (Saminu)

Saminu