logo

HAUSA

Ayyukan rage abubuwa masu gurbata muhalli da Sin ta gudanar sun zama abin misali ga duniya a wannan fanni

2021-11-01 11:18:00 CRI

Tsohon ministan kiyaye muhalli na kasar Faransa Brice Lalonde ya yi nuni da cewa, Sin ta taka muhimmiyar rawa a yayin shawarwari kan sauyin yanayi a tsakanin kasa da kasa, kana burin Sin na kayyade lokacin da yawan sinadarin cabon da ake fitarwa zai kai matsayin koli, da shirinta na samun daidaituwa tsakanin iskar cabon da ake fitarwa da yawan iskar da aka rage ta wasu fasahohi, dukkansu sun burge mutanen duniya.

Mr. Lalonde ya kara da cewa, Sin ta riga ta jagori sauran kasashen duniya wajen tinkarar sauyin yanayi, kuma a halin yanzu ya kamata Sin ta ci gaba da taka irin wannan muhimmiyar rawa, da sa kaimi ga dukkan kasashen duniya su shiga wannan aiki.

Ya ce ayyukan da Sin ta gudanar suna da muhimmanci, kana karfin Sin na raya sha’anin samar da makamashin da ake iya sabunta su shi ma yana da matukar burgewa. (Zainab)