logo

HAUSA

Sakatariyar yada labarai ta White House ta kamu da COVID-19

2021-11-01 11:35:33 CRI

Sakatariyar yada labarai ta White House ta kamu da COVID-19_fororder_211101-US-A2

Sakatariyar yada labarai ta fadar White House ta Amurka Jen Psaki, ta kamu da cutar COVID-19.

Psaki ta ce, da ma dai ta karbi riga-kafi, kuma tana fama da alamomin kamuwa da cutar marasa tsanani. Sannan za ta koma bakin aikinta bayan kwanaki 10 idan ta kammala zaman killace kanta bayan sakamakon gwajinta ya nuna ba ta dauke da cutar.

A halin yanzu, sakatariyar ta soke ziyarar da aka shirya za su yi tare da shugaban Amurka Joe Biden, gabanin tashinsu, inda aka bukaci gwajin gaggawa ga iyalanta, yayin da gwajin da aka yiwa iyalan nata ya nuna suna dauke da kwayar cutar.

Tana daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka kamu da cutar, yayin da jami’i na baya bayan nan da ya harbu da cutar shi ne sakataren tsaron cikin gidan kasar, Alejandro Mayorkas.

Sakatariyar yada labaran ta fadar White House, ta sha ganawa sau da dama da shugaban kasar Amurkan. Biden, wanda shekarunsa ya kai 78. An bayyana cewa yana daga cikin mutanen da suke rukunin wadanda suka fi tsananin barazanar kamuwa da cutar, wanda ya karbi riga-kafin COVID-19 na kamfanin Pfizer kana ya karbi zagaye na uku na riga-kafin. (Ahmad)