logo

HAUSA

An rufe taron G20 na Rome da alkawarin shawo kan tarin kalubalolin duniya

2021-11-01 14:11:00 CRI

An rufe taron G20 na Rome da alkawarin shawo kan tarin kalubalolin duniya_fororder_211101-G20.S3

A jiya Lahadi ne aka rufe taron kungiyar G20 a birnin Rome na Italiya, inda aka fitar da takardar shugabanni ta bayan taron, wadda ke kunshe da alkawarin karfafa matakan bai daya na yaki da annoba, tare da share fage na farfadowar duniya, musamman ma sassa masu rauni.

Shugabannin kasashen duniya masu wadata sun sha alwashin amfani da dukkanin damar da suke da ita, wajen dakile mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifa, da wanzar da farfadowa, tare da kara sanya lura ga manya manyan kalubalolin duniya kamar matsalar katsewar hajojin bukatun al’ummu.

An dai gudanar da taron na yini 2 ne ta yanar gizo da kuma a zahiri, karkashin jagorancin fadar gwamnatin Italiya. An kuma bayyana kasar Indonesia a matsayin wadda za ta karbi shugabancin karba karba na kungiyar tun daga watan Disamban bana.  (Saminu Alhassan)