logo

HAUSA

Jami’an tsaro 3 sun mutu yayin musayar wuta da ‘yan bindiga

2021-10-31 17:20:40 CRI

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta sanar cewa, wasu jami’an tsaro uku sun mutu bayan musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindiga a jahar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar a ranar Alhamis.

Mohammed Shehu, kakakin hukumar ‘yan sandan jahar Zamfara, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, wasu ‘yan bindigar da ba a tantance ko su wane ne ba sun yiwa tawagar rundunar sintirin ta hadin gwiwa dake kumshe da jami’an ‘yan sanda da ‘yan bijilanti kwanton bauna akan wata hanyar da ke karamar hukumar Shinkafi dake jahar a ranar Alhamis.

Mohammed Shehu ya ce, jami’an tsaron sun kwashe sa’o’i suna musayar wuta da ‘yan bindigar, inda suka kashe da dama daga cikin ‘yan bindigar yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.(Ahmad)