logo

HAUSA

Wang Yi: Matakin Amurka ya gurgunta zaman lafiyar Taiwan

2021-10-30 16:12:52 CRI

Jiya Juma’a 29 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya amsa tambayoyin da manema labarai suka gabatar masa kan matakin da wasu kasashe kamar Amurka suka dauka wai suna goyon bayan Taiwan da ya shiga tsarin MDD da harkokin zamantakewar al’ummar kasa da kasa, yayin da yake halartar taron kolin kasashen G20, inda ya bayyana cewa, akwai kasar Sin daya kacal a duniya, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ita ce halastacciyar gwamnati daya tak dake wakiltar ikon mulkin kasar Sin, Taiwan wani bangare ne dake cikin yankin kasar Sin, yanzu haka kasashen duniya sun riga sun cimma matsaya daya kan batun.  

Wang Yi ya jaddada cewa, bai kamata a nuna shakku kan tarihin kasar Sin daya tak a duniya ba, kuma ba zai yiyu a hana yunkurin al’ummun Sinawa da yawansu ya kai biliyan daya da miliyan 400 na ingiza dungulewar kasar Sin ba, babu zabi dake gaban Taiwan, face dungulewa da babban yankin kasar Sin, saboda babu matsayinsa a duniya, sai dai ya kasance a matsayin wani yanki dake cikin kasar Sin.

Wang Yi ya kara da cewa, babban taron MDD ya zartas da kuduri mai lambar 2758 bisa kuru’un neman rinjaye a shekarar 1971, inda aka tsai da kuduri cewa, za a maido da halastacciyar kujerar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD, lamarin da ya tabbatar da matsayin kasar Sin a MDD da kuma hukumomin kasa da kasa.(Jamila)