logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin: Hadin gwiwar MDD da AU a yanzu shi ne mafi muhimmanci fiye da kowane lokaci

2021-10-29 10:27:38 CRI

Wakilin kasar Sin: Hadin gwiwar MDD da AU a yanzu shi ne mafi muhimmanci fiye da kowane lokaci_fororder_i01-UN-hoto

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya bayyana a jiya cewa, hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar tarayyar Afrika AU na da muhimmanci fiye da kowane lokaci, bisa la’akari da gagarumin sauyin da aka samu a fannin siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewar al'umma a duniya da ma Afirka, gami da sabbin kalubalolin da suka kunno kai.

Zhang Jun, ya kuma yi kira ga MDD da AU, da su yi hadin gwiwa a fannoni hudu: Na farko shi ne taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar annobar COVID-19, da taimakawa kasasen Afirka wajen warware manyan matsalolin zaman lafiya da tsaro da suka fuskanta, da taimakawa Afirka wajen tinkarar abubuwan da ke haifar da rikici, da kuma taimakawa kasashen Afirka wajen magance matsalolin dake haifar da rikice-rikice, da kuma yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kara karfin haɗin kan nahiyar.

Ya kara da cewa, Afirka na da al'adar samun ’yancin kai, kuma AU ita ce tutar hadin kan Afirka da dogaro da kai. Don haka ya ce "Muna bukatar mutunta ’yancin kai da shugabancin kasashen Afirka da kuma tallafawa kasashen Afirka wajen bincike da martaba hanyoyin ci gaba da suka dace da yanayin kasashensu.”

Wakilin na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, da kafa wani tsarin tafiyar da harkokin mulki, da tada rikici ko rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen Afirka, da kakkaba sharadi na siyasa don bayar da taimako, da yunkurin amfani da Afirka wajen neman ra'ayin siyasa.

Ya kuma bayyana cewa, Sin da Afirka sun kasance abokai, ’yan uwa kana abokan hadin gwiwa a ko da yaushe. A watan Nuwamba ne, za a yi taro na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a Senegal. Yana mai cewa, kasar Sin za ta yi amfani da wannan dama, wajen taka rawar gani wajen taimakawa Afirka wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da farfadowa bayan COVID-19, da kuma sa kaimi ga kasashen duniya wajen goyon bayan kasashen Afirka. (Ibrahim)