logo

HAUSA

Bunkasa ci gaban bai daya na gabashin Asiya bisa salon cudanyar sassa daban daban

2021-10-29 20:17:15 CRI

Bunkasa ci gaban bai daya na gabashin Asiya bisa salon cudanyar sassa daban daban_fororder_sin

A kwanakin baya ne aka kammala taro na 16 na kasashen gabashin Asiya. A yayin wannan taro da ya gudana ta kafar bidiyo, Sin ta gabatar da wasu shawarwari tare da wasu dabaru, kamar batun hada hannu wuri guda domin yaki da annobar COVID-19, da bunkasa farfadowar tattalin arziki, da ingiza samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da goyon bayan babban ikon kungiyar ASEAN.

Hakika wadannan matakai, baya ga ingiza tasirin hadin kan kasashen gabashin Asiya, suna kuma tabbatar da nasarar aiwatar da manufar cudanyar dukkanin sassa cikin adalci, ta hanyar gudanar da ayyuka a fayyace.  (Saminu)