Ya kamata Amurka ta saurari muryoyi daga taron dandalin Xiangshan
2021-10-28 11:24:07 CRI
A ranar 26 ga wata da dare, an rufe taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Xiangshan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A wajen taron na kwanaki biyu, masana sama da 50 da suka fito daga kasashe fiye da 20 sun yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar dake tsakanin manyan kasashe da tsaron yankin Asiya da tekun Pasifik da cudanyar kasa da kasa da sauransu, wadanda suke ganin cewa, ya kamata a kiyaye cudanyar kasa da kasa da ma hadin gwiwar cin moriyar juna a tsakaninsu, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Sai dai a yayin da masanan kasa da kasa ke kokarin gano bakin zaren warware matsalolin tsaro da ake fuskanta a wajen taron, a ranar 25 ga wata, jiragen ruwa masu daukar jiragen sama na kasar Amurka suka gudanar da atisayen soji tare da jiragen ruwan yaki na kasar Japan a tekun kudancin kasar Sin, matakin da ya tsananta yanayin tsaro na shiyyar.
Yadda aka kira taron dandalin tattaunawar Xiangshan a birnin Beijing ya shaida yadda kasar Sin ke nacewa ga bin manufar hadin gwiwar cin moriyar juna da bada taimakonta ga kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
A yayin da ’yan Adam ke fuskantar kalubalolin tsaro a fadin duniya, ya kamata a kara inganta tsarin kula da harkokin duniya da tsarin cudanyar kasa da kasa da ma hadin gwiwar shiyyoyi daban daban, don shawo kan kalubalolin. Faduwa ta zo daidai da zama da aka gudanar da taron dandalin tattaunawa na Xiangshan, kuma ya kamata Amurka ta saurari muryoyi daga wajen taron. (Lubabatu)