logo

HAUSA

Najeriya ta zama mambar AIIB

2021-10-28 09:48:44 CRI

Najeriya ta zama mambar AIIB_fororder_A01-Nigeria joined AIIB

Wani rahoto ya bayyana cewa, an amince da Najeriya ta zama mambar bankin zuba jarin samar da kayayyakin more rayuwa na Asiya (AIIB), a yayin taron hukumar daraktocin bankin karo na 6 a ranar 27 ga watan Oktoba. Shekaru uku ke nan a jere, AIIB yana samun karin kasashen Afrika cikin mambobinsa.

A shekarar 2020, taron hukumar daraktocin AIIB karo na 5 ya amince da kasar Liberia ta zama mambarsa. A shekarar 2019, a taron AIIB karo na 4 hukumar daraktocin ta amince da kasashen Afrika uku da suka hada da Benin, Djibouti da Rwanda su zama mambobinsa. Kawo yanzu, AIIB ya fadada kawancenta zuwa mambobi kasashen duniya 104, wanda ya kunshi kasashen Afrika 11 da wasu karin kasashe 9 da ake sa ran shigarsu bankin. AIIB ya sana da cewa, amincewar baya bayan nan na kasashen Afrika a matsayin mambobinsa ya kai sama da kaso 60 bisa 100 na adadin GDP nahiyar kana sama da kaso 46 na yawan al’ummar Afrika. (Ahmad)