logo

HAUSA

Masana sun yi hasashen kyakkyawar makoma ga Najeriya game da amfani da tsarin eNaira

2021-10-28 14:08:45 CRI

Masana sun yi hasashen kyakkyawar makoma ga Najeriya game da amfani da tsarin eNaira_fororder_a04-News Analysis

Kwararru a Najeriya sun yi tsokaci cewa, yayin da a kwanan nan kasar ta kaddamar da kudin intanet na eNaira, ana fatan sabon tsarin amfani da kudin kasar na zamani zai taimaka wajen daga matsayin tattalin arzikin kasar mafi yawan al’umma a Afrika, kasancewar matakin zai kara bunkasa kirkire kirkire, da inganta al’amurra ta hanyar bunkasa tsarin hada hadar kudade ta zamani.

A ranar Litinin ne shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da eNaira, wato sabon tsarin amfani da kudin kasar na zamani na babban bankin kasar (CBDC), lamarin da ya baiwa kasar damar zama kasar Afrika ta farko da ta gabatar da tsarin amfani da kudi na zamani kuma daya daga cikin ta farko farko a duniya.

Kwararru a fannin kudi da tattalin arzikin a kasar sun yaba da sabon tsarin da kasar ta bullo da shi, inda suka yi hasashen samun kyakkyawar makoma ga amfani da kudin zamani ga kasar ta yammacin Afrika.

Tope Fasua, mai sharhi kan tattalin arziki, kuma tsohon ma’aikacin banki, ya bayyana cewa, rungumar amfani da kudin zamani abin yabawa ne, yana mai cewa, wani mataki ne da zai dora Najeriyar kan turba mai kyau kasancewar tsarin zai taimakawa tattalin arzikin kasar wajen rage makudan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da takardun kudade Naira na zahiri kana ya shafi ’yan Najeriya da dama dake fannin kudi.

Uche Uwaleke, farfesa a fannin kudi da musayar kudade a jami’ar jihar Nassarawa, dake tsakiyar Najeriya, ya ce kaddamar da eNaira zai iya zama kalubale ga makomar bankunan kasar a nan gaba. (Ahmad)