logo

HAUSA

Kungiyar AU ta dakatar da Sudan daga kasancewa mambar ta

2021-10-28 19:35:09 CRI

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta dakatar da kasancewar Sudan mambar ta, sakamakon tabarbarewar yanayin siyasar kasar.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Laraba, majalissar wanzar da zaman lafiya da tsaron kungiyar AU ta ce, matakin dakatar da Sudan din ya biyo bayan sauyin gwamnati na ranar Litinin, wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, kuma ya yi karan tsaye ga manufofi, da ka’idojin dimokaradiyya da kungiyar AUn ke karewa.  (Saminu)