logo

HAUSA

AU ta yi kira ga EU da ta amince da takardun shaidar yin rigakafin COVID-19 na Afirka

2021-10-27 11:16:02 CRI

AU ta yi kira ga EU da ta amince da takardun shaidar yin rigakafin COVID-19 na Afirka_fororder_211027-yaya 3-AU

Mataimakiyar shugabar kungiyar tarayyar Afirka Monique Nsanzabaganwa ta bukaci kasashen kungiyar Tarayyar Turai, da su kaurace wa manufar kin karbar takardun shaidar yin rigakafin COVID-19 daga nahiyar.

Da take jawabi a wajen bude taron ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai da na kungiyar tarayyar Afirka a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, uwar gida Monique Nsanzabaganwa ta nuna cewa, irin wannan manufa, tana iya shafar aikin yiwa al’ummar nahiyar riga kafi. 

A watan da ya gabata ne dai, Burtaniya ta sanar da manufar kin karbar takardun shaidar yin rigakafin Covid-19 daga nahiyar, wanda hukumomi suka ce, hakan na iya kara shakku ga yin rigakafin.

Kasar Burtaniya dai, ta sanar da jerin sunayen farko na kasashen da ta amince da rigakafin nasu, kuma babu koda guda daga Afirka.

Nsanzabaganwa ta ce, nahiyar tana kallon ’yar uwa nahiyar da kuma goyon bayan kasashe mambobinta, a ci gaba da kiraye-kirayen da kungiyar ke yi, na ganin an yi watsi da hakkin mallakar fasaha, da ke da alaka da allurar COVID-19 da sauran fasahohin kungiyar cinikayya ta duniya.

Ta kuma jaddada mahimmancin samar da alluran rigakafi a duniya, ta yadda duniya baki daya za ta samu garkuwa a yakin da ake yi da cutar ta COVID-19. (Ibahim Yaya)