logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya gana da mataimakin shugaban gwamnatin rikon kwaryar Taliban

2021-10-26 11:19:32 CRI

Ministan wajen Sin ya gana da mataimakin shugaban gwamnatin rikon kwaryar Taliban_fororder_a03-Chinese FM meets acting deputy PM of Taliban interim govt

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da Mullah Abdul Ghani Baradar, mai rikon mukamin mataimakin firaministan gwamnatin rikon kwaryar kungiyar Taliban, a Doha babban birnin kasar Qatar a ranar Litinin.

A lokacin ganawar tasu, Wang ya ce kasar Sin, wadda ba ta taba yin katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Afghanistan ba, kuma ba ta bukatar nuna son zuciya ko neman yin babakere, burinta shi ne manufar kyautata alaka da dukkan al’ummun kasar Afghanistan, da kuma goyon bayan dukkan wani kokari na farfado da zaman lafiya da gina ci gaban kasar. Wang ya bayyana fatansa cewa, gwamnatin Taliban ta kasar Afghanistan za ta cigaba da gudanar da al’amurranta a bayyane, da zaman lafiya, da hada kan dukkan kabilun kasar Afghanistan don yin aiki tare don gina zaman lafiya, da kuma kiyaye hakkokin mata da yara.

Ministan wajen Sin ya gana da mataimakin shugaban gwamnatin rikon kwaryar Taliban_fororder_a03-Chinese FM meets acting deputy PM of Taliban interim govt2

Mista Wang ya jaddada cewa, kungiyar fafutukar musulunci ta gabashin Turkestan (ETIM), kungiyar ta’addanci ta kasa da kasa wanda kwamitin sulhun MDD ya sanya ta cikin jerin sunayen kungiyoyin ta’addanci, ba kawai tana haifar da barazana ga tsaron kasar Sin da yankunanta ba ne, har ma ta jefa zaman lafiya da tsaron kasar Afghanistan cikin hadari na dogon lokaci. Yana fatan kungiyar Taliban ta Afghanistan za ta nisantar kanta da ETIM da sauran kungiyoyin ta’addanci, da kuma daukar kwararan matakai na ganin bayansu.

A nasa bangaren, Baradar ya yiwa Wang Yi bayani game da yanayin da ake ciki a halin yanzu a Afghanistan, inda ya ce gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan tana aiki tukuru domin biyan bukatun al’umma, kuma za ta koyi darasi daga kwarewar da ta samu a tarihinta wajen bin hanyar bunkasa cigaban al’umma bisa dacewa da yanayin kasar. (Ahmad Fagam)