logo

HAUSA

Editan Congo: Dawowa jamhuriyar jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerarta a MDD ya kara karfafa gwiwar kasashen Afirka

2021-10-25 10:18:52 CRI

Editan Congo: Dawowa jamhuriyar jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerarta a MDD ya kara karfafa gwiwar kasashen Afirka_fororder_211025-yaya 1-Editan Congo

Babban editan wata jarida mai samun karbuwa a Jamhuriyar Congo, Bernaard Makiza ya bayyana cewa, dawowa jamhuriyar jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerarta a MDD, wata nasara ce ta diflomasiyya da ta zaburar da kasashen Afirka.

A ranar 25 ga Oktoba, 1971 ne, zaman taro na 26 na babban zauren MDD, ya amince da kuduri mai lamba 2758 tare da babban rinjaye, don dawo wa Jumhuriyar Jama'ar Sin (PRC) halastacciyar kujerarta a MDD tare da amincewa da wakilan gwamnatinta kadai, a matsayin halastattun wakilan kasar Sin a majalisar.

Wannan lamari na tarihi, ya shiga kanun labarai a duniya, ciki har da jaridar La Semaine Africaine ko kuma “Makon Afirka”, daya daga cikin tsoffin jaridun da suka tsira a Afirka ta tsakiya.

A sharhin editan da aka wallafa a ranar 7 ga Nuwamba, 1971, jaridar ta yaba da nasarar diflomasiyyar da kasar Sin ta cimma a shafinta na farko.

Babban editan ya bayyana cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a shekarun 1970 cewa,"Dawo da wannan kujera abu ne da babu makawa. Tabbas ya kamata kasar Sin ta kasance cikin MDD."

Daga cikin kuri'u 76 na amincewa kan kuduri mai lamba 2758, 26 na kasashen Afirka ne. Makiza ya ce, kasar Sin, wacce ita ma ta taba fuskantar mulkin mallaka, tana da buri iri daya da na kasashen Afirka da dama. Hakan ne ya sa Afirka ta ba da gudummawa wajen kafa tarihi, bayan da wasu kasashe suka yi yunkurin karkatar da tsarin tarihi.

Ya ce, "Ga Afirka, kasar Sin kawa ce da za ta taimaka musu wajen kawar da matsalar rashin ci gaba musamman sakamakon mulkin mallaka."

Yayin da ake shirin gudanar da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka shirya yi a karshen wannan shekara a Dakar na kasar Senegal, Makiza ya ce yana da babban fata a kan taron da ma imanin zai haifar da kyakkyawar alakar Sin da Afirka. (Ibrahim Yaya)