logo

HAUSA

Ban Ki-moon: Kasar Sin ta ba da gudummawa don cimma burin MDD

2021-10-25 16:12:40 CRI

Ban Ki-moon: Kasar Sin ta ba da gudummawa don cimma burin MDD_fororder_ban

Yayin wata zantawa da ya yi a baya-bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, tsohon babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya bayyana cewa, kasar Sin ta ba da gudummawa sosai don tabbatar da manufofin MDD.

A cikin shekaru goma da ya yi a matsayin babban sakatare janar, Ban ya shaida faruwar muhimman al'amura da dama, kamar yarjejeniyar Paris da manufofin ci gaba mai dorewa (SDGs) daga cikin muhimman al'amuran duniya.

Ban ya ce, duk wadannan sun samu ne bisa jagoranci mai karfi da sa hannun kasar Sin karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping.(Ibrahim)