logo

HAUSA

MDD: Hari ta sama ya kawo cikas ga jirgin saman aikin jin kai a hanyar Mekelle na Habasha

2021-10-24 16:43:45 CRI

MDD tana nazari game da jirgin samanta a yankin Mekelle na kasar Habasha, bayan wasu hare hare ta sama da suka tilastawa jirgin saman MDDr karkata akalarsa bayan da ya nufi yankin Tigrayan a ranar Juma’a, kamar yadda wata jami’ar MDD ta bayyana.

Kimanin fasinjoji 11 ne ke cikin jirgin saman, kamar yadda Gemma Connell, dake aiki a ofsihin jin kai na MDD ta bayyana. Sai dai babu rahoton wanda ya jikkata.

Wani jirgin saman ayyukan jin kai na MDD da ya tashi daga Addis Ababa da safiyar ranar Juma’a, inda ya koma da baya yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa yankin Mekelle, sakamakon hare hare ta jiragen sama, jami’ar ta kara da cewa, an riga an sanar da gwamnati game da jirgin tun gabanin tashinsa.

Sai dai wannan batu ya haifar da wasu tambayoyi cewa, ko jirgin saman MDDr zai gudanar da aikinsa ne daga babban birnin kasar Habasha zuwa babban birnin Tigrayan.(Ahmad)