logo

HAUSA

Jose Neves ya lashe zaben shugaban kasar Cape Verde

2021-10-23 15:47:13 CRI

Jiya Jumma’a ranar 22 ga wata, hukumar zabe ta kasar Cape Verde wato CNE, ta tabbatar da Jose Maria Neves a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ranar Lahadin da ta gabata.

Jose Neves, tsohon Firaministan kasar Cape Verde da ya samu goyon bayan jam’iyyar African Party for the Independence of Cape Verde, ya lashe zaben ne da kaso 51.75 na kuri’un da aka kada.

Carlos Veiga, shi ma tsohon firaministan kasar Cape Verde, shi ne dan takara da ya zo na biyu a zaben da ya samu goyon bayan jam’iyyar Movement for Democracy, inda ya samu kaso 42.4 na kuri’un.

A cewar shugabar hukumar CNE Maria do Rosario Goncalves, hukumar zaben ta yi ammana cewa, an gudanar da sahihin zabe a ranar 17 ga wata. Haka zalika kuma, tawagar masu sa ido ta kungiyar kawancen raya tattalin arzikin kasashen yammacin duniya wato ECOWAS ta nuna cewa, an gudanar da zaben a kasar Cape Verde yadda ya kamata.

Ana sa ran sabon shugaban kasar zai sha rantsuwar kama aiki a farkon watan Nuwamba mai kamawa.

Jose Maria Neves mai shekaru 61 a duniya ya zama firaministan kasar Cape Verde daga watan Febraren shekarar 2001 zuwa watan Afrilun shekarar 2016.  (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha