logo

HAUSA

Boeing ya yi hasashen yadda kasuwar jiragen sama za ta kasance a nahiyar Afrika nan da shekaru 20

2021-10-22 10:18:54 CRI

Boeing ya yi hasashen yadda kasuwar jiragen sama za ta kasance a nahiyar Afrika nan da shekaru 20_fororder_211022-Faeza2-Boeing

Kamfanin kera jiragen sama na Boeing, ya yi hasashen kamfanonin jiragen saman nahiyar Afrika, za su bukaci sabbin jirage 1,030 zuwa shekarar 2040, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 160, yayin da sauran hidimomi kamar na gyara za su lakume dala biliyan 235.

Kamfanin ya bayyana haka ne a wani bangare na hasashensa na kasuwa na bana, wanda shi ne nazari da ya yi hasashe mai dogon zango, kan bukatar jiragen saman kasuwanci da hidimomi.

A cewar hasashen, jiragen nahiyar Afrika za su karu da kaso 3.6 a kowacce shekara, domin biyan bukatun fasinjojin dake karuwa da kaso 5.4 duk shekara, wanda shi ne adadi mafi yawa na 3 a duniya.

Manajan daraktan sashen kula da cinikayya a yankunan Gabas da tsakiya da Afirka na kamfanin Boeing, Randy Heisey, ya ce nahiyar Afrika na da damarmaki masu kyau na fadada tafiye-tafiye da yawon bude ido, wanda ya zo daidai da karuwar habakar birane da kudin shiga. (Fa’iza Mustapha)