logo

HAUSA

Masu Kudi Na Kasar Amurka Sun Raunata Tsarin Dimokuradiya

2021-10-22 09:06:35 CMG

Masu Kudi Na Kasar Amurka Sun Raunata Tsarin Dimokuradiya_fororder_20211021-sharhi-dimokuradiya-Bello

Kasar Amurka ta kan kalli kanta a matsayin abin koyi a fannin gudanar da tsarin Dimokuradiya, sai dai kuma haskenta ya disashe a wannan lokacin da muke ciki, inda saurin bazuwar cutar COVID-19 a kasar, da tarin mutanen da annobar ta kashe, da tashin gwauron zabo da farashin kayayyaki ya yi a kasar, da rikicin da aka samu tsakanin kabilu da al’ummun kasar, duk wadannan abubuwan suka sanya ake nuna shakku kan yanayin tsarin Dimokuradiya na kasar. Hakika yadda masu kudi na kasar suke babakere a fannin siyasa ya riga ya raunata tsarin Dimokuradiya din kasar, har ma ya sa ya zama abun banza.

Da ma an tsara Dimokuradiya ne don tabbatar da moriyar jama’a da halartarsu cikin harkokin mulki. Sai dai yanzu a kasar Amurka, da kudin al’umma, da ikon mulki, dukkansu sun fada hannun ‘yan tsirarun mutane masu tarin kudi.

Emmanuel Saez, wani shehun malami ne mai nazarin ilimin tattalin arziki, dake aiki a jami’ar California, Berkeley, ta kasar Amurka. A cewar sa, matsakaicin kudin shiga da kashi 10% na al’ummar kasar Amurka suke samu, ya ninka na sauran kashi 90% na jama’ar kasar har fiye da sau 9. Yayin da matsakaicin kudin shiga da mutane masu tarin kudi da yawansu ya kai kashi 0.1% na al’ummar kasar suke samu, ya ninka na kashi 90% na al’ummar kasar fiye da sau 196.

Ban da wannan kuma, su masu kudi na kasar Amurka suna yin amfani da dabaru daban daban, wajen samar da tasiri kan harkokin mulki na kasar. Misali suna ba ‘yan siyasan kasar dimbin kudi don taimaka musu samun nasara a yakin zabe. Kana su kan yi kokarin kulla hulda da ‘yan majalissu, da sanya a lallashe su, domin a tsara dokoki da manufofin da suke bukata. Sa’an nan mutane masu kudi na kasar Amurka suna hadin gwiwa da jam’iyyun siyasa sosai, ta yadda ko jam’iyyar Democratic, ko kuma ta Republican, dukkansu suke nuna fifiko ga kokarin tabbatar da moriyar masu kudi.

A wannan kasa, inda ‘yan tsirarrun mutane masu kudi suke iya tasiri kan harkokin siyasa yadda suka ga dama, ta yaya za a iya kare moriyar mafi yawan jama’a? A wata kasa da ta yi kamar haka, har ma ana iya cewa wai ana samun Dimokuradiyya?

Hakika tsarin jarin hujja yana kara habaka a kasar Amurka, har ma ya zama wani tsarin siyasa da ya kunshi mutane kalilan da suke mallake komai, yayin da mafi yawan mutanen suka rasa damar samun nasara. Wannan shi ne ainihin tsarin da ake bi a kasar Amurka, maimakon Dimokuradiya. (Bello Wang)

Bello