logo

HAUSA

Shugaban Nijar ya yi fatan inganta dangantaka tsakanin Sin da kasarsa

2021-10-21 11:14:01 CRI

Shugaban Nijar ya yi fatan inganta dangantaka tsakanin Sin da kasarsa_fororder_Nijer

Jiya Laraba, shugaban jamhuriyar Nijer Mohamed Bazoum, ya ce kasarsa tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin, domin daga dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Bazoum ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da sabon jakadan kasar Sin a Nijar din Jiang Feng, ke mika takardar wakilcin kasarsa ga shugaban kasar. Mohamed Bazoum ya nuna cewa, kasarsa da kasar Sin, suna da zumunci mai zurfi, kuma, an cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin samar da ababen more rayuwa, man fetur, da kiwon lafiya da sauransu, wadanda suka tallafa wa al’ummomin kasashen biyu kamar yadda ake fata.

Ya ce Nijar tana mai da matukar hankali ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, tana kuma fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin, wajen daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare kuma, Jiang Feng ya ce, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Nijar tana bunkasuwa yadda ya kamata, kuma, bangarorin biyu suna ci gaba da karfafa fahimtar juna a harkokin siyasa a tsakaninsu, lamarin da ya sa, suka cimma sakamako da dama. Ya kara da cewa, bayan barkewar cutar COVID-19, kasashen biyu sun taimaka wa juna, da nuna goyon baya ga juna. (Maryam)