logo

HAUSA

MDD: Ya kamata a jingina duk wani tallafi da za a baiwa Afghanistan da batun kare hakkin matan kasar

2021-10-21 11:10:49 CRI

Mataimakiyar walikin MDD game da harkokin mata na kasar Afghanistan Alison Davidian, ta bukaci sassan kasa da kasa da su jingina duk wani tallafi da za su baiwa Afghanistan da batun kare hakkin matan kasar.

Jami’ar ta ce ya zama wajibi, a kara azama wajen tabbatar da kare hakkokin mata, da daidaiton jinsi a Afghanistan. A kuma tabbatar da cewa tallafin jin kai da za a mika ga kasar, ya isa ga dukkanin mata da mazan kasar.

Davidian na wannan tsokaci ne, yayin wani taro da aka gudanar ta kafar bidiyo game da batutuwan da suka shafi mata, a jajiberin bude muhawarar kwamitin tsaron majalissar, game da mata da zaman lafiya da tsaro.

Jami’ar ta kuma bukaci sassan kasa da kasa, da su tabbatar da gabatar da sako mai karfi, wanda zai nuna manufar su ta bai daya, da za ta karfafa gwiwar kungiyar Taliban, ta yadda za ta rungumi kare hakkokin mata da na sauran sassan al’ummun kasar.  (Saminu)