logo

HAUSA

’Yan sandan Isra’ila sun yi taho mu gama da Falasdinawa a birnin Kudus

2021-10-20 10:32:51 CRI

’Yan sandan Isra’ila sun yi taho mu gama da Falasdinawa a birnin Kudus_fororder_211020-Saminu1-

A daren jiya Talata, ’yan sandan Isra’ila sun yi taho mu gama da Falasdinawa, a wajen tsohon birnin gabashin Kudus. Cikin wata sanarwa da suka fitar, ’yan sandan Isra’ila sun ce Falasdinawa masu zanga zanga, sun rika jifan motocin bas da duwatsu, a kusa da kofar Damascus ta tsohon birnin, kuma tuni aka damke 22 daga cikin wadanda ake zargi.

A nata bangare kuwa, kungiyar jin kai ta Red Crescent tsagin Falasdinawa, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, an yiwa Falasdinawa 17 jinyar raunuka da suka ji, sakamakon duka, da harsasan roba, da barkonon tsohuwa da ’yan sandan Isra’ila suka rika harba musu.

Lamarin ya auku ne yayin da mabiya addinin musulunci ke bikin mauludi na bana. Kuma Falasdinawa sun zargi ’yan sandan Isra’ila da haddasa tashin hankalin, bayan da suka hana su taruwa a kusa da kofar Damascus ta tsohon birnin, inda suka jima suna taruwa a lokutan bukukuwan su.

Ana ci gaba da zaman dar dar cikin kwanakin baya bayan nan tsakanin sassan biyu, inda a wadannan darare, Falasdinawa da ’yan sandan Isra’ila kan baiwa hamata iska a gabashin birnin na Kudus.     (Saminu)