logo

HAUSA

COVID-19 da kiyayya, sun sanya Amurkawa ‘yan Asiya neman maganin ciwon damuwa

2021-10-20 14:50:51 CRI

COVID-19 da kiyayya, sun sanya Amurkawa ‘yan Asiya neman maganin ciwon damuwa_fororder_src=http___news_chinaxiaokang_com_uploads_image_20210223_1614055325244936_jpg&refer=http___news_chinaxiaokang

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa, cutar COVID-19 da laifuffukan dake da alaka da kiyayya, sun sanya karin Amurkawa ‘yan asalin Asiya neman maganin ciwon dake da alaka da damuwa. A cewar kungiyar masu kula da matsalolin kwakwalwa ta Amurkawa ‘yan asalin Asiya, sama da kaso 40 na Amurkawa ‘yan Asiya, sun shiga cikin yanayi na damuwa ko zullumi a lokacin barkewar annobar, idan aka kwatanta da kaso 10 da ake da su kafin barkewarta. (Fa’iza Mustapha)