logo

HAUSA

Matsi ba ya taba karkatar da hankalin kasar Sin daga burin da ta sanya gaba

2021-10-19 17:27:28 CRI

Matsi ba ya taba karkatar da hankalin kasar Sin daga burin da ta sanya gaba_fororder_1019-1

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce, tattalin arzikin kasar ya kara farfadowa a rubu’i na uku na wannan shekarar, tana mai cewa ma’auni ya nuna cewa tattalin arzikin yana cikin kyakkyawan yanayi.

Shin ko kasashen dake daukar kasar Sin a matsayin abokiyar adawa, suna la’akari da yadda kasar ke dukufa wajen kyautata tattalin arziki da kuma walwalar jama’arta? Yayin da suke can suna cece-kuce da katsalandan cikin harkokin gidan kasar Sin, tuni ita ta yi nisa wajen zage damtse a kokarinta na tsaya da kafarta. Baya ga haka, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta, da matsin da ake ciki, tana kara fadada taimakonta ga kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika.

Duk da adawar da ake nuna mata, kasar Sin ba ta bari su yi tasiri ga shirye- shiryenta, haka kuma ba sa wani tasiri a idon kasashen da ake yi dominsu, wato goga mata bakin fenti a wajensu, domin lamarin ya zama tamkar kaikayi koma kan mashekiya, duba da yadda ita Sin ta yi zarra ta kowane bangare, misali ta shawo kan annobar COVID-19, yayin da har yanzu manyan kasashen ke fama da ita, tun bayan barkewar cutar kuma, harkoki a kasar ke farfadowa, yayin da har yanzu kasashen ke fafutukar tsayawa da kafarsu. Maimakon su tsaya su nazarci matsalolin dake tattare da su, sai suka mayar da hankali wajen neman matsawa Sin da yi mata hassada.

Kamata ya yi ci gaban da Sin take samu ta kowacce fuska, ta kasance tamkar izini, ta yadda za su mayar da hankalin wajen inganta ci gaban tattalin arzikinsu da zamantakewar al’umma da hada hannu wajen ciyar da duniya gaba. Tuni dai Sin ta bayar da gudunmuwarta ga ci gaban tattalin arzikin duniya da farfadowar harkoki har ma da kokarin dakile cutar COVID-19, amma ita kadai ba za ta iya ceton duniya ba. Dole sai an kawar da sabani da bambance-bambace don a gudu tare a tsira tare. (Faeza Mustapha)