logo

HAUSA

Amurka ba za ta shiga tattaunawar da Rasha ta kira game da Afghanistan ba

2021-10-19 10:36:42 CRI

Amurka ba za ta shiga tattaunawar da Rasha ta kira game da Afghanistan ba_fororder_1019-Saminu2-Ned Price

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price, ya ce Amurka ba za ta shiga tattaunawar da Rasha ta kira game da batutuwan da suka shafi Afghanistan ba.

Ned Price, wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a jiya Litinin, ya ce Amurka ba za ta halarci tattaunawar ba saboda wasu kalubale na tsare tsare, duk da cewa tana goyon bayan tattaunawar da za a yi gobe Laraba.

A Juma’ar karshen makon jiya ne dai jakadan Rasha a kasar Afghanistan Zamir Kabulov, ya ce kasarsa ta gayyaci Amurka da ta halarci tattaunawar birnin Moscow, wadda za ta maida hankali ga matakan sake ginawa, da ayyukan jin kai bayan kawo karshen tashe tashen hankula a Afghanistan.

Rasha ta gayyaci wakilan kungiyar Taliban zuwa taron da aka tsara gudanarwa gobe. Tun a shekarar 2017 ne dai aka fara gudanar da taron da Rasha ke shiryawa game da Afghanistan, karkashin lemar sassa 6 masu wakiltar Rasha, da Afghanistan, da Sin, da Pakistan, da Iran da India. (Saminu)