logo

HAUSA

MDD na bincike game da harin sama a Mekelle na yankin Tigray

2021-10-19 09:57:07 CRI

MDD na bincike game da harin sama a Mekelle na yankin Tigray_fororder_1019-Saminu1-Habasha

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce majalissar ta damu matuka game da rahotannin dake cewa an yi luguden wuka ta sama, kan fararen hula a Mekelle dake yankin Tigray na kasar Habasha.

Mr. Dujarric wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, ya ce MDD na nazari game da tabarbarewar yanayin tsaro a yankin Tigray, yayin da karancin kayayyakin bukatun yau da kullum, musamman ma kudade da makamashi, suka gurgunta ayyukan tallafin jin kai a yankin. Lamarin da ya jefa a kalla fararen hula sama da 400,000 cikin wani yanayi mai kama da fari.

Gwamnatin Habasha dai ta yi watsi da zargin cewa dakarunta ne suka kaddamar da harin ta sama a Mekelle. To sai dai kuma rahotanni na cewa, ’yan tawayen yankin ba su da makaman yaki ta sama, don haka ba zai yiwu su kaddamar da irin wannan hari ba.   (Saminu)