logo

HAUSA

Adadin mutanen da suka mutu a harin ‘yan bindiga a jihar Sokoton Najeriya ya kai 43

2021-10-19 09:31:30 CRI

Hukumomi a Najeriya sun sanar da cewa, adadin mutanen da suka mutu a harin da ‘yan bindiga suka kai wani gari a jihar Sokoto dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ya karu zuwa 43 yayin da aka gano karin gawarwaki.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana hakan a sanarwar baya bayan nan da yammacin ranar Litinin, a cewar gwamnan, a daren Lahadi ne wasu gungun ‘yan bindiga suka kaddamar da hari a garin Goronyo, helkwatar karamar hukumar Goronyo dake jihar.

Gwamnan ya bukaci a tura karin jami’an tsaro zuwa jihar da kuma karin kayan aiki don samun nasarar dakile kalubalolin tsaro dake addabar jihar.

A wata sanarwa daga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da mummunan harin da ‘yan bindigar suka kaddamar a jihar Sokoto, ya ce lokacin kaddamar da irin wadannan munanan laifuffuka zai zo karshe.

Ya ce a halin yanzu ‘yan bindigar suna fuskantar matsin lamba mafi tsanani sakamakon matakan da dakarun tsaron kasar ke dauka ta jiragen sama da kuma ta kasa a dukkan wuraren fakewarsu.(Ahmad)