logo

HAUSA

COVID-19 ta yi sanadin mutuwar tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell

2021-10-19 10:06:56 CRI

COVID-19 ta yi sanadin mutuwar tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell_fororder_1019-Faiza1-Collin Powell

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka kuma bakar fata na farko da ya rike mukamin wato Colin Powell, ya rasu jiya yana da shekaru 84, biyo bayan kamuwa da cutar COVID-19.

Wata sanarwa da iyalansa suka fitar, ta ruwaito cewa, Colin Powell wanda kuma ya rike mukamin babban hafsan sojin kasar, kafin ya zama babban jami’in diflomasiyyar kasar, ya rasu ne da safiyar jiya bayan kuma ya karbi cikakkiyar allurar riga kafin COVID-19.

A matsayinsa na kwararren soja, Colin Powell ya zama baAmurke bakar fata na farko da ya zama mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro a karshen wa’adin mulkin Ronald Reagan, haka kuma bakar fata na farko mafi kankantar shekaru da ya rike mukamin babban hafsan soji karkashin shugabancin George H. W. Bush.

Sai dai kuma, ya yi fice a matsayin mafi jawo rudani a lokacin da yake sakataren harkokin wajen Amurka karkashin shugabancin George W. Bush, tsakanin watan Junairun 2001 da Junairun 2005, bisa la’akari da yadda ya ingiza kutsen da Amurka ta yi wa Iraqi a shekarar 2005, bisa hujjar cewa, kasar dake gabas ta tsakiya ta mallaki makaman kare dangi da har yanzu ba a tabbatar ba. (Fa’iza Mustapha)