logo

HAUSA

Babban sakataren kungiyar ITU: Sin za ta bayar da gudummawa ga bunkasuwar ITU

2021-10-19 10:18:34 CRI

Babban sakataren kungiyar ITU: Sin za ta bayar da gudummawa ga bunkasuwar ITU_fororder_ITU

Kwanan baya, babban sakataren kungiyar sadarwa ta duniya wato ITU Zhao Houlin ya bayyana cewa, bayan dawowar matsayin kasar Sin a kungiyar ITU, kasar ta sami gagarumin ci gaba a fannin sadarwa, a nan gaba kuma, kasar Sin za ta ba da karin gudummawa ga bunkasuwar kungiyar ITU.

Yana mai cewa,

“Yanzu, mun fara aiwatar da shirin taimakawa kasar Uganda a aikin gina ababen more rayuwa na harkokin sadarwa, kuma, an tsara wannan shiri ne bisa goyon bayan Asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa wanda kasar Sin ta kafa, kuma muna fatan za a ci gaba da inganta ayyuka a wannan fanni. A fannin fasaha kuma, na yi imanin cewa, ko wace sabuwar fasaha za ta ba da tasiri ga kungiyar ta ITU, shi ya sa, ina fatan kasar Sin za ta taimaka wa dukkanin bil Adama, a aikin habaka albarkatun sararin samaniya, da teku mai zurfi, yayin da kasar ke bayar da gudummawar ta a fannin raya sabbin fasahohi.” (Maryam Yang)