logo

HAUSA

Bach ya bayyana kwarin gwiwarsa game da nasarar gasar Olympic ta birnin Beijing dake tafe

2021-10-18 09:49:54 CRI

Bach ya bayyana kwarin gwiwarsa game da nasarar gasar Olympic ta birnin Beijing dake tafe_fororder_1018-Saminu2-Bach

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta kasa da kasa ko IOC a takaice Thomas Bach, ya ce shirye-shiryen gasar Olympics ta lokacin hunturu dake tafe a birnin Beijing na gudana yadda ya kamata. Kuma Sin ya kammala shirya dukkanin filayen da wasannin gasar za su gudana tun watannin baya, wanda hakan abu ne mai matukar burgewa.

Bach wanda ya yi wannan bayani yayin zantawarsa da majiyar gungun kamfanonin radio da talabijin na kasar Sin CMG a kasar Girka, ya ce tuni mashirya gasar na kasar Sin suka fara gwajin wasanni a wuraren da aka tanada, kuma ’yan wasa dake gwajin sun nuna gamsuwa matuka, don haka IOC ke jinjinawa nasarar tsarin da aka aiwatar.

Bach ya kara da cewa, babban aikin dake gaban IOC shi ne tsarawa, da kuma gudanar da wasannin, tare da aiwatar da matakan killace ’yan wasa. Ya ce tuni suka fara zantawa da hukumar shirya gasar wasannin Olympic na lokacin hunturu na Beijing, da hukumomin Sin, da kwararru na kasa da kasa, don tabbatar da kowa ya nishadantu da gasar cikin yanayi na tsaro.  (Saminu)