logo

HAUSA

Wakilan Syria za su gana a Geneva don tattauna batun kudin mulkin kasa

2021-10-18 10:05:17 CRI

Wakilan Syria za su gana a Geneva don tattauna batun kudin mulkin kasa_fororder_1018-Ahmad1-Sham

Ana sa ran a yau Litinin mambobin karamin kwamitin tsara kundin mulkin kasar Syria za su bude sabon zagayen tattaunawa kan batun kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda jakadan MDD ya bayyana.

Wakilin musamman na MDD a kasar Syria, Geir O. Pedersen, ya fadawa taron manema labarai a ranar Lahadi cewa, bangarorin sun amince za su fara tsara daftarin kundin tsarin mulkin kasar don aiwatar da sauye sauye.

Jakadan MDD ya fadawa manema labarai cewa yanayin bukatar tallafin jinkan bil adama da yanayin tattalin arziki a Syria na kara shiga cikin matsanancin hali. Ya ce akwai sama da mutane miliyan 13 a Syria dake bukatar tallafin jinkai.

Kwamitin shirya kundin tsarin mulkin na Syria ya kunshi wakilan gwamnatin kasar, da ’yan adawa, da kungiyoyin fararen hula, wadanda aka kaddamar da su a hukumance a Geneva a ranar 30 ga watan Oktoban 2019 domin su rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar mai fama da yaki. (Ahmad)