logo

HAUSA

Mutane 3 sun mutu a sanadiyar fashewar tankar mai arewacin Najeriya

2021-10-14 10:08:23 CRI

Hukumomi sun bayyana cewa mutane 3 ne suka mutu sannan wasu mutum biyu sun samu raunuka a lokacin da wata tankar man fetur ta yi bindiga a jahar Adamawa dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Mohammed Sulaiman, babban sakataren hukumar kiyaye haddura ta jahar Adamawa, ya bayyanawa manema labarai a Yola, babban birnin jahar cewa, mutanen da lamarin ya rutsa da su sun kone kurmus bayan da tankar mai ta kama da wuta a yankin Mubi dake jahar da sanyin safiyar ranar Laraba.

Jami’in ya bukaci ’yan kasuwar dake hada hadar mai a jahar da su guji yin aiki a lokutan da ba su dace ba domin kaucewa fuskantar haddura. (Ahmad)